Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kaduna ta yabawa Buhari kan shirin daukar ma’aikata

Published

on

Kwamishiniyar ma’aikatar inganta rayuwar al’umma da raya karkara ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba ta ce shirin daukan ma’aikata dubu a kowace karamar hukuma da gwamnatin tarayya ta bullo dashi zai taimaka gaya musamman ga masu karamin karfi.

Hajiya Hafsat Baba ta bayyana haka ne lokacin kaddamar da kwamitin mutum ashirin da za su gudanar da aikin zakulo wadanda za su amfana da shirin a jihar kaduna.

Ka zalika ta ce kwamitin da aka kafa karkashin ofishinta ya hada da masu ruwa da tsaki ta kowane bangare da za su yi aiki domin tabbatar da tafi da shi yadda ya kamata ba tare da tauye wani bangare ba.

Karin labarai:

Ganduje ya aikewa majalisar dokoki sunaye mutum biyu – KANSIEC

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga a wasu kananan hukumomi

Kwamishiniyar ta cigaba da cewa za su bi tsarin da karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi Festus Keyamo ya bayar wajen zabo mutanen da za su amfana da aikin.

Hafsat Baba ta kara da cewa za su yi amfani da ‘yan jaridu wajen gudanar da aikin domin tabbatar da sanya gaskiya a cikin sa.

A karshe ta shawarci al’umma musamman matasa da basu da aikin yi, su yi kokarin cin gajiyar shirin na gwamnatin tarayya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!