Labarai
Gwamnatin Kaduna zata baiwa daliban sakandire ilimi kyauta
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewar, nan bada jimawa ba zata aike da kudirin doka ga majalisar dokoki ta jihar don fafa shirin bada ilimi kyauta kuma tilas ga daliban makarantun sakandire na jihar
Mataimakiyar Gwamnan jihar ta Kaduna Hadiza Balarabe ta bayyana hakan a yayin dake gabatar da kunshin daftarin kasafin kudin badi ga majalisar dokoki ta jihar ta Kaduna wanda ya kai fiye da Naira biliyan dari biyu.
“Daga shekara ta dubu biyu da Ashirin 2020 kowanne dalibin makarantar na jhar nan zai ci gajiyar karatu kyauta na shekaru goma sha biyu 12’’ A cewar Hadiza Balarabe
Yan bindiga dadi sunyi garkuwa da mutane 8 a jihar Kaduna
Gwamnatin Kaduna za ta daukaka kara kan hukuncin El Zazzaki
Yayin da take bayani kan yadda kasafin kudin zai kasance, Mataimakiyar gwamnan wace ita ce take jan ragamar gwamnantin jihar ta Kaduna a halin yanzu, ta ce za’a kasha fiye da Naira biliyan dari da casa’in akan manyan ayyuka, yayin d akuma za’a kashe fiye da Naira.biliyan 67 a ayyukan yau da kullum,tan amai cewar a kulluma gwamnatin jihar na sanya kudorori da manufofin alummar jihar akan gaba fiye da komai.
A dai cikin kunshin daftarin kasafin kudin badi an kebewa bangarorin Ilimi da kiwon lafiya Naira biliyan dari da Arba’in 140, wanda ya kai kasha 73 cikin 100 na kasafin kudin shekara ta 2020.