Labarai
Gwamnatin Kano ta kara sassauta dokar kulle
Gwamnatin Kano ta kara ranar Litinin a cikin ranakun sararawa a fadin jihar.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Lahadi, ta bakin mai magana da yawun gwamnati Abba Anwar.
Yanzu haka dai ranakun sararawa hudu ake da su a Kano, da suka hadar da Litinin, Laraba, Juma’a da kuma Lahadi.
A cikin sanarwar, gwamnatin Kano ta ce za a rika zirga-zirga daga karfe shida na safiya zuwa shida na yamma a cikin ranaku hudun da aka ware.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ja hankalin al’ummar jihar da su cigaba da bawa gwamnati goyon baya, a yakin da take yi na dakile cutar Covid-19.
Sannan gwamnatin ta kuma gargadi mutane da su cigaba da amfani da takunkumin rufe hanci da baki, bayar da tazara, wanke hannu a ko yaushe da sinadarin wanke hannu.
Umar Ganduje ya kuma bukaci da a cigaba da bin dokokin gwamnati a kasuwanni da sauran wuraren taron jama’a, yayin da gwamnati ke cigaba da lalubo hanyoyin dakile yaduwar cutar Covid-19 a fadin jihar.
You must be logged in to post a comment Login