Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta rufe makarantun lafiya masu zaman kansu guda biyu

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu makarantu masu zaman kansu guda biyu da ke horas da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Nasarawa, bisa zargin karya ƙa’idojin gudanarwa da rashin cika sharuddan da ake buƙata.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta fitar, inda ta ce bincike ya nuna cewa makarantun ba su samu amincewa daga ma’aikatar da kuma hukumomin da ke kula da ilimin kiwon lafiya ba, sannan suna da ƙarancin ƙwararrun malamai, kayan aiki da muhimman abubuwan more koyo.

Ma’aikatar ta ce ta ɗauki matakin ne domin kare ɗalibai da iyaye tare da tabbatar da ingancin horas da ma’aikatan lafiya a jihar. Ta kuma gargaɗi masu irin waɗannan makarantu da su tabbatar sun bi dukkan ƙa’idoji da dokokin da suka shafi gudanar da cibiyoyinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!