Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta tabbatar da samun ci gaba a manyan ayyukan raya kasa

Published

on

Ma’aikatar bibiya da lura da aiyyukan  Gwamnatin Jihar Kano, ta tabbatar da samun  ci gaba a wasu manyan ayyukan raya kasa da ake gudanarwa a fadin birnin Kano, biyo  bayan ziyarar aiwatar da su karkashin jagorancin Kwamishinan ma’aikatar , Kwamared Nura  Iro Ma’aji Sumaila.

Ma’aikatar, ta ce  aikin gyaran Babbar Masallacin Juma’a na Kano ya kai matakin karshe, Sai dai bayan ruwan sama na farko a bana, an samu zubar  ruwa a wasu sassan rufin masallacin, da Sarkin Ladanan Kano ya gabatar da korafin gyaran hakan inda  Kwamishinan ya tabbatar da cewa za a sanar da dan kwangilar domin gyara matsalar kafin kammala aikin.

Kwamitin bibiyar ayyukan ya kuma duba aikin fadadawa  da gyaran Asibitin Yara na Hasiya Bayero da ke Kofar Kudu, ciki har da cibiyar kula da masu cutar sikila ta Abba Care, sashen kula da masu fama da rashin abinci mai gina jiki da kuma bangaren raba magunguna kyauta.

Kwamishinan ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na Gidan Dan Masani, inda ya bayyana gamsuwa da aikin wajen kana ya  duba wasu ayyuka da suka hada da gina katanga da  saka fitilu masu amfani da  hasken rana a Dutsen Dala, gyaran Kwalejin Addinin Musulunci ta Abdullahi Bayero da Makarantar larabci ta  (SAS), da kuma shimfida kwalta a hanyoyin Sokoto Road, Iyaka Road, Guda Abdullahi Road, Justice Dahiru Mustapha Road da hanyar Unguwa Uku zuwa Zaria Road ta ‘Yan Awaki.

Nura Iro Ma’aji Sumaila, ya  duba manyan ayyuka guda 12 da darajar su ta haura sama da  naira biliyan 21.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!