Labarai
Gwamnatin Kano za ta kashe fiye da biliyan uku a ayyukan raya kasa
Gwamnatin jihar Kano za ta kashe sama da naira biliyan uku domin gudanar da aiyyukan raya kasa daban -daban a ma’aikatun da suka hadar da ta Ruwa da ma’aikatar Kasa da tsare-tsare da fannin ilimi da suaran su.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamred Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishin sa yayin da yake bayyana sahalewar da majalisar zartaswa ta jihar Kano a zamanta na biyar, karkashin jagorancin gwamnan Jihar Kano da ta yi na kudaden don gudanar da aiyyukan.
Muhammad Garba, ya ce, majalisar zartaswar ta sahale wa ma’aikatar albarkatun Ruwa kudi na naira biliyan biyu, don samar da sinadaran tsaftace ruwa, da samar da wadataccen ruwa a fadin jihar Kano.
Haka kuma ya ce, a wani shiri na hadaka tsakanin tarayyar Turai wato EU, da asusun tallafawa kananan yara da ilimi na majalisar dinkin duniya watau UNICEF, na tsaftace ruwa da muhalli gwamnatin jihar ta bada nata kason miliyan 150, don gudanar da aikin.
Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar zartaswar ta kuma amince da sakin kudi har naira miliyan 89, don daga darajar karamin asibitin Kafin mai Yaki, dake karamar hukumar Kiru, tare da samar da kayan aiki da Kawata shi don inganta harkokin lafiya a kananan hukumomi tare da rage cunkoso a cikin asibitocin cikin birni.
Wakilinmu Aminu Halilu Tudun wada, ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma sahale da a kashe kimanin naira miliyan 441 da naira miliyan 323 domin gudanar da wasu aiyyukan da suka hada da gyaran motocin daukar dalibai 57 da ciyar da dalibai a makarantun kwana tare da samar da kwamfutoci da Internet a ma’aikatun gwamnati gami da bada horon sanin makamar aiki ga ma’aikatan hukumar ilimi ta jihar Kano.