Labarai
Gwamnatin Kano za ta kashe sama da miliyan 98 a bangaren wasanni
Majalisar zartarwa ta jihar Kano, ta amince da kashe naira miliyan 82, don siyan kayan wasanni ga kungiyoyin Kwallon kafa na jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishin yada labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba ya sanyawa hannu, inda sanarwar ta ce Majalisar ta amince da ware kudin tare da kashe su ne a yayin zaman da ta yi a larabar makon da ya gabata.
Majalisa ta amince Ganduje ya nada sabbin masu ba shi shawara
Kano ba ta bukatar kafa rundunar tsaro -Ganduje
Ta cikin Sanarwar, Muhammad Garba ya ce an ware kudin ne don siyan riguna da kwallayen kafa da sauran kayan amfani a bagaren na tamola.
Malam Muhammad Garba, ya kara da cewa kayan za a rabawa kungiyoyi guda dubu daya da dari bakwai da casa’in da biyu dake fadin jihar Kano.
Ana sa ran ko wa ce kungiya zata samu rigunan kwallo da jakunkuna da littafin rubutu da kuma kwallaye.
You must be logged in to post a comment Login