Labaran Kano
Gwamnatin Kano za ta rage kasafin kudin 2020
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata rage kasafin kudin shekarar 2020 da kaso 30 cikin 100.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin wani taron manema labarai da fadarsa ta shirya a Kano.
Gwamnan ya ce sun dauki matakin ne sakamakon kalubalen da ya tunkaro saboda cutar Coronavirus.
A cewar gwamnan nan gaba kadan zasu mika bukatar hakan gaban majalisar dokokin jihar domin sake yin nazari da kuma sahalewa.
Abdullahi Umar Ganduje ya kuma yabawa ‘yan jaridu bisa yadda suke bayar da gudun mowa wajen wayar da kan jama’a game da cutar Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login