ilimi
Gwamnatin Katsina ta sanar da ranar komawar ɗalibai makaranta
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da ranar uku ga watan Oktoba a matsayin ranar da makarantun gwamnati da masu zaman kan su za su koma karatu a fadin jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar Malam Sani Danjuma ya fitar.
A cewarsa, komawa makarantar zai bada dama wajen cike gurbin zangon karatu na uku na shekarar 2020 da 2021 musamman a yankunan da suke fuskantar matsalar tsaro a jihar.
Sanarwar ta ce, kwamishinan ilimin jihar Dakta Badamasi Lawal ya tabbatar da cewa dukannin daliban makarantun kwana da jeka-ka-dawo za su ci gaba da karatu a ranar 4 ga watan Oktoba.
Tun da fari dai an tsara komawar dalibai makaranta a jihar a ranar 13 ga watan Satumbar da muke ciki, sai dai an ɗage shi ne don daidaita jadawalin karatu
You must be logged in to post a comment Login