Labarai
Gwamnatin Katsina ta za ta dauki tsauraran matakai kan ‘yan ta’adda
Gwamnatin jihar Katsina ta ce daga yanzu babu sauran sasanci tsakaninta da masu aikata ta’addanci a jihar.
Haka zalika gwamnatin ta Katsina ta nemi gwamnatin tarayya da ta dauki matakai kan matsalolin ‘yan bindigar da suka addabi wasu jihohin Arewa ciki har da Katsinan.
Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Muhammad Inuwa a zantaawrsa da Freedom radio ya ce sun lura cewa ‘yan ta’addar da suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da su a baya sun koma ruwa.
Ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki mataki mai tsauri a kan ‘yan ta’addar, la’akari da yadda suke neman mamaye wasu jihohin.
“A tunkari mutanen nan gaba-daya, a shiga Katsina, zamfara, Kaduna, Neja a tabbatar an yi musu zobe, ina me tabbatar maka yin hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar ta’addancin nan”. In ji shi
A cewarsa ya fi kyautuwa a kara kaimi a yaki da ta’addanci, domin mutanen yankunan da abun ya shafa su samu su koma muhallansu.
You must be logged in to post a comment Login