Addini
Gwamnatin Najeriya na nuna fifiko tsakanin Musulmai da Kiristoci – MURIC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi gwamnatin Najeriya da nuna fifiko tsakanin Musulmai da Kiristoci a ƙasar.
MURIC ta yi wannan kiran ne bayan ta samu rahotannin cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar gina wani katafaren coci da za kashe wa naira biliyan 25 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
A wata sanarwa da MURIC ta aike wa BBC, shugaban ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya kuma nuna takaici kan yadda gwamnatin ta tallafa wa waɗanda rikici ya shafa a jihar Filato da naira biliyan 2, ba tare da ta yi irin hakan a jihohin Sakkwato, Borno, Kebbi da Zamfara ba, da su ma suke fama da matsalolin tsaro.
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayanin dalilin da ya sa ake nuna wannan fifiko. Musulmai a Najeriya ba su cancanci haka ba…,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin Najeriyar ta ware irin waɗannan kuɗaɗe na kimanin naira biliyan 25, da kuma fili ga Musulman ƙasar domin su ma su gina katafaren masallaci a filin jirgin.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Wannan haƙƙin mu ne. Kuma ya kamata a ba mu.”
You must be logged in to post a comment Login