Connect with us

Labarai

Gwamnati ta haramta amfani da lakabin “Dr” ga masu digirin girmamawa

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa amfani da lakabin “Dr” a gaban sunayensu a hukumance ko a harkokin aiki da ilimi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da yake bayani kan wasu matakan da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da su.

A cewar gwamnatin, duk wanda ya gabatar da digirin girmamawa a matsayin cikakken digirin ilimi, za a ɗauki hakan a matsayin damfarar ilimi, wanda zai iya jawo hukunci tare da ɓata suna.

 

Alausa ya ce sabon tsarin zai kawo ƙarshen yadda wasu jami’o’i ke bayar da digirin girmamawa bisa la’akari da siyasa ko kuɗi maimakon cancanta.
Ya ƙara da cewa, “Masu digirin girmamawa ba za su ƙara sanya ‘Dr’ a gaban sunayensu ba. Maimakon haka, za su rubuta cikakken nau’in digirin a ƙarshen sunayensu.”

Ministan ya bayar da misalai kamar: Chief Louis Clark, D.Lit. (Honoris Causa) ko Mrs Miriam Adamu, LL.D (Hons.)
Bugu da ƙari, sabon tsarin ya takaita nau’o’in digirin girmamawa da jami’o’in Nijeriya za su bayar zuwa guda huɗu kacal, ciki har da Doctor of Laws (LL.D) da Doctor of Science (D.Sc).

Hakazalika, gwamnati ta hana jami’o’in da ba su da shirye-shiryen bayar da digirin PhD bayar da digirin girmamawa.
Alausa ya ce Ma’aikatar Ilimi tare da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) za su sa ido domin tabbatar da an bi wannan sabuwar doka yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!