Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta ce ta baiwa jihohin kasar nan tallafin tiriliyan daya a shekaru biyu
Gwamnatin tarayya ta ce jihohin kasar nan talatin da shida sun karbi tallafin sama da naira tiriliyan daya daga wajen gwamnatin tarayya tsakanin shekarar dubu biyu da sha biyar zuwa shekarar da ta wuce.
Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a garin Lokoja babban birnin jihar Kogi.
Ya ce kudaden sun hada da: tallafin kasafin kudi da kudaden Paris club da kudaden rarar man fetur da dai sauransu.
Farfesa Yemi Osinbajo wanda ke jawabin a wajen taron saka hannayen jari da tattalin arziki wanda gwamnatin jihar Kogi ta shirya ya ce, an baiwa jihohin kudaden ne domin ba su damar gudanar da ayyukan raya kasa.
Mataimakin shugaban kasar ya ce mafi yawa daga cikin kudaden mallakin jihohin ne wadanda aka dawo musu da shi daga kungiyar ba da lamuni ta Paris club da kuma kudaden rarar man fetur.