Labarai
Gwamnatin tarayya za ta bude filayen jiragen saman Kano da Abuja
Gwamnatin tarayya ta ce za ta bude filayen jiragen saman kasar nan a ranar takwas ga watan Yulin 2020.
Ministan sufurin sama Hadi Sirika ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, inda ya ce filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da na Nnamdi Azikwe da ke Abuja za su fara aiki ne ranar takwas ga watan na Yuli.
I am glad to announce that Abuja & Lagos airports will resume domestic operations on the 8th of July, 2020. Kano, Port Harcourt, Owerri & Maiduguri to resume on the 11th. Other airports on the 15th. Date for international to be announced in due course. Bear with us, please 🇳🇬🙏🏽🇳🇬
— Hadi Sirika (@hadisirika) July 1, 2020
A cewar sa filayen jiragen sama na Kano, Port Harcourt, Owerri da Maiduguri za a bude su ne ranar 11 ga watan Yulin.
Wannan na zuwa ne bayan sama da watanni uku da gwamnatin tarayya ta rufe filayen jiragen sama, sakamakon annobar Covid-19.
Hadi Sirika ya ce za a bude sauran filayen jiragen saman a ranar 15 ga watan Yuli, sai dai batun fara jigilar jirage zuwa kasashen waje sai a nan gaba kadan gwamnati za ta sanar.
You must be logged in to post a comment Login