Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe wasu manyan jagororin yan bindiga

Published

on

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka  wasu manyan jagororin ‘yan bindiga biyu, Anaruwa da Gomina, tare da wasu mutum bakwai a jerin hare-haren da aka gudanar cikin kwanaki uku a jihohin Zamfara da Katsina.

 

Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar, Sashe na 8 na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, da ya fitar aka raba ga manema labarai

 

An kuma bayyana cewa Anaruwa ƙanin shahararren jagoran ‘yan bindiga ne, Kachalla Idi Aiki.

 

Laftanar Kanal Olaniyi ya ƙara da cewa a farkon farmakin, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan a kan hanyar Bagega zuwa Anka, inda aka yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!