Kasuwanci
Gwamnatin Zamfara ta fitar da sabbin dokokin don magance matsalar tsaro
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya sanya hannu kan dokar haramta sayar da biredi maras dauke da sunan kamfaninsa da ake naɗewa cikin leda da kuma hana sayar da fiye da lita 50 na man Fetur da kuma haramta amfani da gilashin mota mai duhu a jihar.
Gwamnan ya sa hannu kan dokar ne a Laraba makon nan a gidan gwamnatin jhar da ke birnin Gusau.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris, ya fitar.
Sanarwar ta ruwaito cewa dokar za ta yi maganin matsalolin da aka bayyana suna janyo ƙalubalen tsaro a jihar.
haka kuma ta cikin sanarwar ya kara da cewa an yi kaddamar da dokar ne saboda hare-haren baya-bayan nan da aka kai wasu yankuna a sassan jihar.
You must be logged in to post a comment Login