Labarai
Gwamnonin Arewa sun goyi bayan ci gaba da rufe makarantu
Kungiyar gwamnonin arewacin kasar nan ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin tarayya kan matakin da ta dauka na ci gaba da garkame makarantu musamman na sakandare tare da dakatar da rubuta jarabawar kammala makarantun sakandare ta WAECC.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar kwamishinonin ilimin jihohin arewacin kasar na 36 suka fitar bayan da suka kammala taron su ta kan Internet.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kuma kwamishin ilimin jihar Kaduna Dr. Shehu Usman Muhammad yana mai cewa gwamnatin tarayya ta dauki wannan mataki ne don kare lafiyar daliban.
Sanarwar ta kuma baiwa ministan ilimi na kasar shawara da ya tattauna da kwamishinonin ilimi jihohin kasar nan don samo hanyar da za’a bi wajen bude makarantun cikin sauki da kuma tabbatar da tsabtar makarantun kafin bude su.
Haka kuma ta cikin sanarwar kungiyar ta yabawa matakin da gwamnonin arewacin kasar nan suka dauka na mayar da almajirai garuruwan su.
Cikin kwamishinonin ilimin da suka halarci taron akwai na jihar Kaduna da na Baushi da Gombe da Niger da Nasarawa da Adamawa da Taraba sai kuma Jihar Kogi da Kwara da Katsina da nan Kano sai Borno da Jihar Jigawa.
You must be logged in to post a comment Login