Labarai
Babu ranar bude jami’o’i – ASUU
Kungiyar malaman jami’o’I ta Najeriya (ASUU) ta ce ba za su koma aji ba, ko da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin bude makarantu, yayin da ake fama da annobar Covid-19.
Shugaban kungiyar, Boidun Ogunyemi a wata hira da manema labarai, ya sake jaddada shawarar da suka bawa gwamnatin Najeriya na kada ta bude makarantu har zuwa shekarar 2021.
Ranar 19 ga watan Maris ne gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin a rufe dukkanin jami’o’in kasar hadi da makarantun sakandire da kuma firamare, bayan da aka samu bullar cutar Coronavirus a kasar.
Sai dai bayan kwanaki kadan da bayar da umarnin ne, ASUU ta fara yajin aikin sai baba ta gani, wanda ta ce har yanzu tana kan bakarta.
ASUU ta ce ta shiga yajin aikin ne saboda shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na hana albashi ga mambobinta da suka yi watsi da sabon tsarin biyan albashin bai daya na IPPIS da gwamnatin ta bullo da shi.
Duk da cewa a yanzu gwamnatin tarayya ta ba da ka’idojin da ta ke son a yi amfani da su ga daliban da za su kammala makaranta a matakan firamare da na sakandire, sai dai babu abinda aka ce game da jami’o’in Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login