Labarai
Hisba ta cafke wasu ‘yan mata a Kano
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wasu ‘yan mata masu kananan shekaru da ake zargi da yawon ta zubar.
Tun da fari dai hukumar ta chafke wata mata ne tare da ‘yan mata biyar masu kananan shekarun, da kuma wani jariri, wanda ta ce kannen ta ne da kuma danta.
Ta ce, ta kuma debo su ne tun daga N’Djamena na kasar Chadi suka kuma yada zango a jihar Borno.
Ta kara da cewa, rashin gata da wanda zai iya kula da tarin ‘yan matan ne ya sanya ta debo su zuwa nan Najeriya don yin sana’ar da zasu dauki nauyin kansu.
Matar ta ce tun daga lokacin da iyayen su suka rasu, suka rasa tudun dafawa kasancewar basu da kowa, a don haka yaga babu wata dabara da ta rage musu sai zuwa nan Najeriya don kama sana’a.
Hukumar ta kuma chafke wata Budurwa wadda ta ce ta zo ne daga jihar Zamfara ne don shiga harkar Film amma ta bige da yawon ta zubar.
Bama wuce gona da iri a ayyukan mu Inji Hisbah
Aikin Allah: Hisbah ta yi rabon tallafi
Hisbah ta ƙulla yarjejeniya da ƴan kasuwar Kwanar Gafan
Budurwar ta kuma ce ta taho da sanin mahaifiyar ta sai dai ‘yan Film din sun ki daukar ta kasancewar babu wata shaida da ta nuna cewa iyayen ta sun amince da ta yi Film din.
Sai dai ta ce, dama tun kafin tahowar ta, mahaifin ta ya shaida mata cewa sai ya sa an Kama ta.
Baya ga wannan ma dai hukumar ta cafke wata mata mai suna Mairo Muhammad mazauniyar unguwar Sharada a nan Kano, wadda ake zargi da ta’ammali da wani Boka, don samun biyan bukata.
Tun da fari dai jami’an hukumar sun sami rahoton cewa matar ta kai kawar ta gurin mutumin ne don taimaka mata ta fannin kasuwanci, kasancewar ita tana da rariyar hannun.
Sai dai Mairo Muhammad ta musanta cewa mutumin Boka ne, kawai dai yana bayar da magani ne.
You must be logged in to post a comment Login