Labarai
Hukumar Hisbah ta ziyarci makarantar ‘yan mari ta zamani
Babban kwamandan hukumar ta jihar Kano Sheik Harun Muhad Sani Ibn Sina da kuma baban daraktan hukumar Dr, Aliyu Musa Kibiya sun kai ziyarar aiki makarantar ‘yan Mari ta zamani dake karamar hukumar Kura anan jihar Kano wanda Asusun tallafawa na Annur ya kafa.
Makarantar ‘yan Marin ta zamani wanda Dr, Aliyu Musa Kibiya ya asasa da nufin karfafa samar da ingantaccen ilimi mussaman ma na Al-qur’ani mai girma don taimakawa a kokarin da gwamnati ke yi na ganin ana bada ilimin Al-qur’ani ta hanyar data dace a jihar Kano.
Haka zalika Tsangayar ko makarantar ‘Yan marin irin ta ce ta farko a jihar Kano da aka taba kafawa ta zamani.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar ta Hisbah Lawal Ibrahim Fagge \ya sanya hannu cewa, tsangayar na da ajujuwa guda 27 da dakunan kwana na dalibai 35 da masallaci.
Hisbah na shirin kara inganta ayyukanta a kananan hukumomi
Laifin iyaye ne ke haifar da mace-macen aure -Hisbah
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben barasa 196,400
Ana dai kyautata zaton cewar a kwanan ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai kaddamar da Tsangayar ta zamani a cikin wannan shekarar yayin da kuma za’a koma karatu gadan-gadan nan bada jimawa ba.