Connect with us

Labarai

Za a samu katsewar lantarki a Kano da kewaye – TCN

Published

on

Hukumar rarraba wutar lantarki ta Najeriya TCN ta ce za a gudanar da wani aikin gyaran cibiyar raba wutar lantarki da ta shafi Kano da wasu jihohin arewacin kasar a ranar Lahadi 28 ga watan Yunin 2026.

Cikin wata sanar da daraktan ya da labaran hukumar, Ndidi Mbah ya fitar ya ce za a gudanar da gyaran domin inganta aikin rarraba wutar lantarkin.

Ya ce katsewar za ta shafi aikin rarraba wutar kamfanonin KEDCO da wasu ɓangarorin kamfanin rarraba wuta na Jos (JEDC) da na Yola (YEDC) da na Yobe (YEDC) da ke samar da wuta ga kwastominsa na Kano da Katsina da Jigawa da kuma garin Azare na jihar Bauchi.

Sauran garuruwan da matsalar za ta shafa sun haɗa da Nguru na jihar Yobe da garin Gazaoua na Jamhuriyar Nijar.

TCN ta kuma nemi afuwar al’umomin waɗannan yankuna tare da alkawarta cewa za a maida wutar da zarar an kammala aikin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!