Labarai
Iyalai da dama sun rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a Damaturu

Iyalai da dama sun rasa matsugunansu bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya a wasu sassan birnin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun ce ambaliyar ta mamaye gidajensu a ranar Asabar, lamarin da ya tilasta wa iyalai da dama komawa gidajen ‘yan uwa ko gine-ginen gwamnati domin samun mafaka.
Wani mazaunin unguwar Malari, Malam Bulama Jalaluddeen, ya ce ambaliyar ta lalata gidaje da bayan-gida, yana mai zargin rashin magudanan ruwa ne ke haddasa maimaituwar matsalar.
Haka kuma, wani mazaunin Abbari Sabon Kwalta, Modu Adamu, ya ce wasu iyalai sun kwana a waje, yayin da wasu ma suka bar gidajensu gaba ɗaya saboda ambaliyar da ke maimaituwa duk shekara.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin, ta na mai cewa ambaliyar ta shafi ƙananan hukumomin Damaturu, Nguru, Machina da Bursari.
Hukumar ta ce ta tura tawagar tantance barnar domin ƙididdige gidajen da suka lalace da yawan mutanen da abin ya shafa, tare da shawarci jama’a su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa, su nisanci magudanan ruwa, kuma su kiyaye dokokin lafiya domin hana yaduwar cututtukan da ruwa kan haddasa.
You must be logged in to post a comment Login