Labarai
Iyaye su umarci ‘ya’yansu sauraron Rediyo don koyon karatu
Wani malamin makarantar Sakandare a nan Kano ya ja hankalin iyaye wajen ganin sun sanya ‘ya’yansu suna sauararon shirye-shiryen koyar da karatu da ake gabatarwa a gidajen rediyo, a sakamakon hutun da aka bayar don kaucewa yaduwar cutar Covid-19 a Kano.
Malam Nura Muhammad ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radiyo wanda ya tattauna kan shirin koyar da daliban ta kafar yada labarai da dan majalisar Wakilai mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano Sha’aban Ibrahim Sharada ya dauki nauyi.
Nura Muhammada ya kuma kara da cewar duba da koma bayan da daliban ka iya samu a bangaren karatun na su sanadiyyar rashin zuwa makarantar ya sa suka zabo wasu daga cikin muhimman darussa guda shida, da suka hadar da lissafi da Ingilishi, don kara zaburar da su.
A na sa bangaren wani makusancin dan majalisar mai suna Alhaji Abubakar Kingibe, cewa ya yi sun samar da tsrin ne don amfanar da al’ummar jihar Kano ta fannin ilimin.
Ya kuma shawarci dabilan da su mayar da hankali wajen sauraron shirin da ake gudanarwa domin bunkasa fahimtarsu.
You must be logged in to post a comment Login