Coronavirus
Jami’o’I na gwaje-gwajen kimiyya don dakile Corona a Najeriya
Hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC ta ce, jami’o’in gwamnatin tarayya da masu zaman kan su talatin da biyu ne suka fara gwaje-gwajen kimiyya daban-daban, da nufin lalubo hanyoyin magance cutar Corona.
Babban sakataren hukumar ferfesa Abubakar Rasheed wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Sulaiman Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin tarraya Abuja.
A cewar sa, gwaje-gwajen kimiyar da jami’o’in suka fara hanya ce na samar da maganin yakar cutar corona, wacce ta adabi duk duniya tun daga bara har kawo wannan lokaci.
Ya kara da cewa, nan da watan Oktoba, jami’o’in za su kawo sakamakon gwaje-gwajen kimiyyar da suka gudanar, don fara gwadawa akan masu dauke da cutar.
You must be logged in to post a comment Login