Coronavirus
Jigawa ta rage kasafin kudi saboda Corona
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da rage kasafin kudin jihar na wannan shekara ta 2020, daga naira billiyan 150 zuwa naira biliyan 124 domin gwamnatin ta samu damar gudanar da ayyukanta a cikin wannan yanayi na annobar COVID-19.
Kakakin majalisar dokokin jihar Honourable Idris Garba Jahun ne ya bayyana hakan a yau Alhamis jim kadan bayan gudanar da wasu gyare-gyare da majalisar tayi a cikin kasafin kudin wannan shekara ta 2020.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya turawa majalisar dokokin jihar kudurin neman rage kasafin kudin na bana.
A cikin takardar gwamna Badaru ya bayyanawa majalisar cewa yin hakan ya zama dole a sakamakon halin da ake ciki a yanzu.
Labarai masu alaka:
Sama da mutum 2000 aka yiwa gwajin cutar Covid-19 a Jigawa
COVID19: Gwamnatin Jigawa ta bayar da umarnin a bude kasuwannin jihar
You must be logged in to post a comment Login