Labarai
Jihar Kano ta samu sarakuna masu biyayya- Alhaji Usman Alhaji
Sakataren gwamnatun jihar Kano Alhaji Usman Alhaji yace gwamnatin jihar Kano ya ce ,jihar Kano ta samu sarakuna masu biyayya da rikon Amana.
Alhaji Usman Alhaji yace babu tantama sabbin sarakuna na Bichi da Kano za su yi wa gwamnatin Kano biyayya.
Haka kuma sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi wasikar shedar nadi a hannun Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa manyan baki daga sassan jihar Kano da kuma sarakunan Gaya da Karaye da kuma na Rano duk sun halacci bikin.
You must be logged in to post a comment Login