Labaran Wasanni
Jinya: Francis Uzoho ya dawo fagen wasa

Mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Francis Uzoho ya buga wasa na farko bayan ya shafe sama da shekara daya yana jinya bisa rauni da ya sama a kafarsa.
Uzoho dai ya samu rauni a kafarsa yayin da Najeriya take fafatawa da Brazil a wani wasan sada zumunta a kasar Singapore.
Dan wasan yanzu haka yana taka leda a kungiyar kwallon kafa ta APOEL Nicosia dake kasar Cyprus.
Ya kuma taka rawar gani a wasan farko bayan dawowarsa da kungiyar ta yi nasara kan PAEEK da ci uku da nema a gasar Cypriot Cup.
You must be logged in to post a comment Login