Labarai
Kadan cikin al’amuran annoba da suka faru a bara
Rahotanni sun nuna cewa jihohi shida da suka hada da Borno, Yobe, Katsina, Gombe, Taraba da kuma nan Kano su ke da kashi 84 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar a kananan hukumomi 15, haka kuma ko wace jiha ta bayar da bayanai kan mutane fiye da 200 da suka kamu da cutar.
Mutane kimanin biyar sun mutu a jihar Kano bayan da kimanin 189 su ka kamu da cutar kwalara ko amai da gudawa, a kananan hukumomi 20 na jihar, inda daga cikinsu mutane 184 su ka warke.
Cutar ta fara kama mutane ne tun daga watan Afirilu zuwa Nuwamba.
A watan Afrilun shekarar da ta gabata ne dai aka sanar da bullar cutar amai da gudawa a Danbatta, wadda daga nan kuma sai ta bulla a kananan hukumomin Gwarzo, Dawakin Kudu da kuma wasu kananan hukumomin cikin birni, da suka hadar da Dala, Ungoggo, Municipal, sai kuma Tarauni.
Sai dai a duk shekara a kan samu barkewar cutar kwalara, wadda wasu ke alakantawa da rashin tsaftar muhalli musamman a lokacin damuna, da kuma yadda jama’a ke zubar da shara barkatai, yin bahaya a fili, da rashin sarrafa abinci ta hanya mai tsafta, wadanda dukkansu ke yada cutar a tsakanin jama’a.
A nan Kano dai lalurar ta fi ƙamari a garin Tamburawa dake ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, inda aka samu asarar rayuka.
Malam Ahmad Hamisu daya daga cikin mazauna garin na Tamburawa, ya bayyana yadda suka riski lamarin.
A gefe guda su ma wadanda suka rasa ƴan uwansu sakamakon bullar cutar ta amai da gudawa sun bayyana alhininsu kamar haka.
Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa shi ne Kwamishinan lafiya na jihar Kano, ya bayyana adadin mutanen da suka kamu da wannan cuta da adadin wadanda suka mutu.
Daga ƙasashen ƙetare kuwa, a cikin watan Maris din shekarar ta 2022 an samu bullar cutar Kyandar Birrai a wasu ƙasashen Turai da Amurka, kuma wannan shi ne karo na farko da aka samu bullar cutar a yankunan.
Inda aka tabbatar da cewa mutane kusan dubu tamanin da biyar suka kamu da ita, yayin da kusan dari biyu da hamsin suka mutu.
Baya ga hakan, cutar ta ɓulla a Afirka, inda ta shiga Afirka ta Tsakiya da Afrika ta Kudu, haka abin ya ci gaba har ta zo nan Najeriya, inda aka tabbatar da kamuwar mutane dari da tara, sannan mutane biyu suka mutu.
You must be logged in to post a comment Login