Manyan Labarai
Kai tsaye: ‘Yan bindiga sun hallaka mutane a Zamfara
Hukumomin tsaro sun tabbatar da mutuwar mutane 20 a garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara.
Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya ce, maharan sun kai harin ne bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato kamar yadda ya yiwa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba karin bayani.
Shehu Muhammad ya ce, tuni suka baza jami’an tsaro don gano wadanda suka yi kisan don fuskantar hukunci.
Jihar Zamfara dai na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindinga.
Gwamnatin Jigawa ta kashe miliyan 80 wajen sayen madara
Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe naira miliyan tamanin wajen sayo madarar tamowa.
Gwamnatin jihar ta ce, ta sayo akalla katan dubu uku da dari shida da arba’in na madarar don rabawa yaran da suka kamu da cutar.
Yayin rabon madarar sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abdulkadir Fanini ya ce, ko wane katan din madarar ya kama naira dubu ashirin da biyu da dari biyu da ashirin da biyu.
Ku kasance da mu a labaran Mu Leka Mu Gano da karfe 7 na dare, don jin ci gaban labarin.
Elrufa’i ya gargadi kamfanin kwashe shara na jihar
Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi kamfanin tsaftar muhalli na jihar.
Kwamishinan muhalli na jihar Ibrahim Hussaini ya ce kamfanin Cape-Gate da ke lura da tsaftar muhalli na neman shafa musu kashin kaji.
Kamfanin dai ya zargi gwamnati da ƙin biyansa haƙƙoƙinsa lamarin da ya sanya ya gaza biyan ma’aikatansa kuɗaɗensu.
A cewar kwamishinan gwamnatin jihar tana biyan kamfanin kuɗaɗe bisa yarjejeniyar da suka cimma.
Sai dai ya ce, “kamfanin na bin ƙananan hukumomi kuɗin wata biyu, inda ya ke bin gwamnatin jiha kuɗin wata uku” kuma hakan bai ci karo da yarjejeniyar da ke tsakaninsu ba a cewar sa.
#ENDSARS: An kafa kwamitin binciken rikicin zanga-zanga a Kano
Rundunar ƴan sandan Kano ta kafa kwamitin bincike kan rikicin da aka samu a unguwar Sabon Gari.
Kwamishinan ƴan sandan Kano Habu Sani Ahmed ya ce, mutane 6 ne suka samu rauni a rikicin, cikin har da baturen ƴan sanda.
Ranar Talata ne aka samu arangama tsakanin masu zanga-zangar #EndSars da wasu ƴan daba a Kano.
An sanya ranar komawa makaranta a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya ranar 25 ga watan Oktoba da muke ciki domin komawa makaranta.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar Bala Ibrahim Mamsa ya shaida wa Freedom Radio cewa sun yi tsare-tsare domin komawar daliban.
Ɗalibai a jihar sun shafe sama da watanni bakwai cikin hutu dalilin cutar Corona.
Ƴan aji ɗaya zuwa uku na Firamare za su riƙa zuwa makaranta da safe.
Aji huɗu zuwa zuwa biyar kuma da yamma, ƴan ƙaramar Sakandire da safe, babbar Sakandire kuma da yamma.
Ganduje ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 64
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 64 a duniya.
Mai taimakawa gwamna Ganduje kan kafafan sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ya wallafa sakon taya murna a madadin gwamnan ta shafinsa na Twitter.
Happy birthday to the Former Governor of State @KwankwasoRM on behalf of the @GovUmarGanduje and People’s of Kano State. pic.twitter.com/8ol0bTjZZa
— Abubakar Aminu Ibrah (@aaibrahm) October 21, 2020
You must be logged in to post a comment Login