Labaran Wasanni
Kamfanin hannun jari na Bahrain Investcorp na dab da siye AC Milan
Kamfanin zuba hannun jari na ƙasar Bahrain , Investcorp na cigaba da tattaunawa da kamfanin ƙasar Amurka na Elliot , Mamallakan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan dake ƙasar Italiya , kan siyan tawagar.
Rahotanni daga ƙasar ta Italiya daga Jaridu da majiyoyi daban -daban, musamman ma Calciomercato , sun tabbatar da cewar tuni tattaunawa tayi nisa tsakanin ɓangarorin biyu don siye ƙungiyar.
Shafin Twitter na ‘Milan Eye on Twitter’ ya ruwaito cewar kamfanin na Investcorp na bukatar kammala cinikin tare da mallakar ƙungiyar a ƙarshen watan Afrilu ko farkon Mayu.
Tuni dai kamfanin suka bayyana cewar zasu cigaba da aiki da jami’in tsare tsare kana Daraktan wasanni na tawagar , tsohon Kyaftin kuma gwarzon ƙungiyar Paolo Maldini.
Haka zalika rahotanni sun cigaba da alaƙanta sabbin masu son mallakar ƙungiyar, da ‘yan wasa irin su Riyard Mahrez da Christopher Nkunku sai Raheem Sterling da Sebastian Haller.
You must be logged in to post a comment Login