Labarai
Kamfanin KEDCO Ya Dakatar Da Dage Wutar Latarki a Wasu Kananan Hukumomin Jihar Kano: KNHA
Majalisar dokokin jihar Kano, ta bukaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta umarci kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO da ya dakatar da dage wuta daga Turakun wasu kananan hukumomin jihar da suke tsaka da yi.
Majalisar ta bukaci hakan a zamanta na yau Talata 23/04/2024, biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar Kiru Usman Abubakar Tasi’u ya gabatar.
Da ya ke gabatar da kudurin dan majalisar na Kiru, ya ce yanzu haka jami’an na KEDCO sun dage fiye da Turakun wuta 150 ba tare da sanar da mazauna yankunan ba, don haka ya kamata gwamnati ta umarci kamfanin ya mayar musu da wutar ba tare da bata lokaci ba.
Da ya ke goyon bayan kudurin, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo, Alhaji Aminu Sa’adu, ya bayyana damuwa bisa yadda kamfanin na KEDCO ke yin shakulatun bangaro wajen kulawa da bukatar al’umma.
You must be logged in to post a comment Login