Addini
Kano: an zargi kwamitin abincin musabaqa da karkatar da kudin masu girki
Wasu mata da su ka gudanar da kwantiragin girke-girken abinci a yayin gasar musabakar Alqur’ani wanda aka kammala a baya-bayan nan a Kano sun koka kan yadda suka dace kwamitin kula da abinci na gasar ya zambace su wajen basu abin da bai taka kara ya karya ba.
Gamayyar matan sun ce, sun kwashe tsawon kwanaki goma sha daya suna gudanar girkin abinci, amma bayan kammala musabaqar sai kawai aka basu naira dubu goma, wanda suka ce yayi kadan da yawa.
A bangare guda sun kuma zargi kwamitin kula da abinci na gasar musabaqar da danne musu wasu kudade naira dubu dari da su k ace mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya basu.
A zantawa da wasu daga cikin matan su ka yi da tashar freedom radio, sun ce, kwamitin abincin ya karbi gudunmawa mai yawa da sunan su, amma kuma ko da sisin kwabo ba a basu a ciki ba.
Malama Amina Umar wadda ita ce ta jagoranci matan, ta ce, ba za su yadda da sallamar naira dubu goma-goma ba a aikin kwanaki goma sha daya.
Sai dai da ya ke mai martani, Alhaji Abubakar Na’abba wanda shi ne sakataren kwamitin kula da Abincin, ya musanta cewa an bai wa matan naira dubu goma ne kacal, yana mai cewa, kudaden da aka basu ya kai naira dubu goma sha daya da dari biyar .
‘‘A duk kwanaki goma sha daya da su ka yi suna zuwa aikin dafa abinci, mun rika basu naira dari biyar-biyar duk rana, saboda haka su ce wai dubu goma kawai mu ka basu, wannan ba gaskiya bane’’ a cewar sakataren kwamitin kula da abincin musabaqar.
You must be logged in to post a comment Login