Labarai
Kano: Mutane 167 ne suka kamu cutar fitsarin jini a mako guda
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce, kawo yanzu mutane 167 ne suka kamu da cutar nan da ta ɓulla a wasu yankunan jihar.
A wata zanta wa da Freedom Radio, Daraktan lura da cutuka na ma’aikatar Dr. Bashir Lawan, ya ce, tuni aka ƙara samar da asibitoci guda takwas domin lura da waɗanda suka kamu da cutar, wadda ya ce ana zargin tana da alaƙa da guba.
Asibitocin sun haɗa da, Asibitin zana, da asibitin koyarwa na Aminu Kano sai asibitin Ƙwararru na Murtala.
Sauran su ne asibitin Waziri Shehu Giɗaɗo, da kuma asibitin Sheikh Jidda da kuma babban asibitin garin Rano da wasu asibitoci biyu a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Dr. Bashir ya ƙara da cewa, yanzu haka cutar ta mamayi ƙananan hukumomi takwas da suka haɗa da ƙaramar hukumar Gwale da Birnin da Kewaye.
Sauran su ne ƙananan hukumomin Dala da kuma Fagge da Bunkure, sai Dawakin Tofa da Gwarzo.
You must be logged in to post a comment Login