Labarai
Kano Pillars ta musanta labarin ƙonewar motarta
Ƙungiyar Kano Pillars, ta musanta labarin ƙonewar motar ƴan wasanta a ranar Jumma’a.
Mai magana da yawun ƙungiyar Lirwanu Idris Malikawa Garu, ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
Ya ce, “Ina tabbatar muku da cewar labarin da aka yaɗa, na cewa motarmu ta ƙone a Unguwar Bawa dake yankin ƙaramar hukumar Madobi, ba gaskiya bane”.
Ya ci gaba da cewa, “Tayar Motar ce kawai ta kama hayaƙi sakamakon matsalolin da motar take ciki”.
“Yanzu haka ƴan wasa da muƙarraban ƙungiyar suna cikin ƙoshin lafiya, kuma maganar da muke da kai sun isa jihar Nassarawa lafiya”.
Malikawa yace, biyo bayan tattaunawa tsakanin shugaban ƙungiyar ta Kano Pillars da shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, tuni Motar hukumar ta kwashi ƴan wasan na Pillars tare da wucewa dasu zuwa jihar Benue don buga wasan Mako 11 a gasar Firimiya ta kasa NPFL.
Da yammacin Jumu’a ne dai wasu jaridu suka riƙa bada labarin cewa motar ƴan wasan Kano Pillars ɗin ta ƙone ƙurmus.
A ranar Alhamis 18 ga Fabrairu 2021 ne, Motar tawagar Wikki Tourist ta kama da wuta tare da ƙonewa ƙurmus a kan hanyar su ta zuwa wasa da Dakkada FC.
You must be logged in to post a comment Login