Kiwon Lafiya
Kano: Red Cross ta yi tsokaci kan Coronavirus
Kungiyar bada agajin gaggawa ta RED CROSS tayi kira ga al’ummar kasar nan dasu kara kaimi wajen kula da tsaftar muhallin su domin kare kansu daga kamuwa da cutar Coronavirus da cutar Lassa.
Jami’in kula da lafiya na kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross reshen jihar Kano Salisu Garba Ahmad ne ya bayyana hakan, lokacin taron wayar da kai da kungiyar dake rajin samarda ayyukan yi da hadin gwiwar gidauniyar Mailemo suka shirya.
Salisu Garba Ahmad ya kara da cewa matukar mutane basu dauki matakan kare Kansu daga wadannan cututtuka ba musamman wajen tsaftace muhallan su da kuma kaucewa duk wasu hanyoyin da zasu iya kawo cutar ba babu shakka cutar zata cigaba da samun gindin zama a tsakanin mutane.
A nasa jawabin shugaban kungiyar samar da ayyukan yi reshen jihar Kano Abubakar Umar Barkama cewa yayi sun dauki matakin shirya taron ne domin su wayar da kan mutane musamman akan matsalolin da ake fama dasu a bangaren lafiya anan Najeriya.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa wakilan kungiyoyi da dama ne suka halarci taron, inda masana kiwon lafiya suka gudanar da makala kan yadda za a magance matsalar kamuwa da cutar coronavirus da cutar Lassa a Najeriya.
Karin labarai:
Musulmai sun yi taron addu’a kan Coronavirus a Kano
Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano
You must be logged in to post a comment Login