Manyan Labarai
Kasar nan na fuskantar matsalolin dake da alaka da Corona – Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce kasar nan na fuskantar matsaloli da ke da alaka da annobar corona.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan jiya a Abuja lokacin da yake jawabi kan Karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka samu a kasar nan.
Ya ce, shugaba Buhari na kokarin ganin an cimma muradan karni ne, ba wai yana nufin matsantawa ga al’umma ba kamar yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta.
Malam Garba Shehu ya kara da cewa, a yanzu kasar nan na yin yaiki da abubuwa da dama a lokaci guda da suka hadar da matsalar tsaro da ambaliyar ruwa da harkar man fetur baya ga annobar corona da ake tsaka da yaki da ita.
Yana mai cewa kowacce gwamnati mai manufa na kokarin ta samarwa al’ummarta mafita da ci gaba.
You must be logged in to post a comment Login