Labarai
Katsina: Mutanen gari sun dakile yunkurin ‘yan bindiga na kai hari musu hari

Mazauna garin Gurbi da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina sun dakile yunkurin ‘yan bindiga na shiga garinsu domin kai hari.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun iso da yamma, amma jama’ar gari sun taru tare da tare hanyarsu, lamarin da ya hana su shiga cikin garin.
Rahotanni sun ce bayan da ‘yan bindigar suka kasa shiga garin ne kuma suka bude musu wuta tare da kashe sama da mutum 10 a yankin Nagodi.
Majiyar ta kuma ce tun kafin harin sun sanar da jami’an tsaro bayan samun bayanan sirri, amma ba a samu dauki ba.
Har zuwa wannan lokacin, rundunar ‘yan sanda da ofishin kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa ba.
You must be logged in to post a comment Login