Labarai
Kwamitin nazari kan kafa yan sandan jihohi ya gabatar da tsarin sanya ido mai ƙarfi

Kwamitin da ke nazarin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi ya gabatar da tsarin sanya ido mai ƙarfi domin kare tsarin daga tasirin siyasa da matsin lamba.
Rahoton kwamitin ya ce dole ne a samar da tsarin sanya ido mai matakai da dama, domin tabbatar da cewa rundunar za ta yi aiki ga al’umma ba tare da biyayya ga ‘yan siyasa ba.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar kafa hukumar kula da ‘yan sandan jihohi a kowace jiha, wadda za ta kula da ɗaukar aiki, ladabtarwa da kuma sa ido kan ayyukan rundunar.
You must be logged in to post a comment Login