Labarai
Killace kai da hana Sallah a cikin jama’a lokacin Annoba dai -dai ne a Musulunci
Babban Limamin Masallacin jumma’a na Alfurkan Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar , yace Killace kai da kauracewa al’umma, da karbar shawarwari na ma’aikatan lafiya da hukumomi dai -dai ne , a cikin koyar wa ta addinin Musulunci.
Dr Bashir Aliyu Umar , yace kasancewar addinin Islama tsari ne na rayuwa ba wai kawai addini ba, ya shirya komai daki – daki da tsari na gudanar da mu’amala lokacin da Annoba ta sauka , don dakile yaduwa, kula da lafiya da tsare rayuka na al’umma tare da dukiya.
Malamin wanda ya bayyana haka a wata hira ta musamman da tashar Freedom Rediyo, ya kafa misalai , da Alkur’ani mai girma da Hadisai na Manzon Allah , wanda suka yi kira da Killace kai , tare da hana taro shiga gari ko al’umma , a wajen addini da sauran al’amurra yau da kullum, wanda tsarin shari’a ya aminta dashi a matsayin babbar lalura.
Shehin Malamin, yace bai kamata al’umma su dinga karyata Annoba ba, da yin halin ko in kula ta hanyar amfani da Addini, wajen yin biris da ka’idoji na killacewa wanda Musulunci ya yi horo dashi da kuma fatwa da dama akai.
Bugu da kari Malamin ,yace labarin da ake ta yadawa na cewar Yahudawa ne da Nasara suka kirkiri cutar don hana aiyyukan Ibadar Musulunci, labari ne mara tushe ballantana makama, kasancewar Turawa da Yahudawa na kan gaba -gaba wadan da cutar ta fi yiwa illa.
Dr Bashir Aliyu Umar, ya kuma yi kira da al’umma da su koma ga Allah, tare da tuba kasancewar sai an saba masa ko an kauce fadin sa, Annoba ke sauka ga al’umma wanda su suka jawo ta da kansu sakamakon aiyyukan da suke aikatawa.
Ya kara da shawartar al’umma da su bi dukkanin matakai da shawarwari da ma’aikatan Lafiya da dangogin su suka bayar, tare da bin umarnin hukumomi don ganin an dakile ko kawar da cutar a fadin duniya.
You must be logged in to post a comment Login