Labarai
Ko kun san hanyar shiga Aljanna cikin sauki a lokacin azumin Ramadan?
Shugaban Gidauniyar tallafawa Marayu da gajiyayyu ta Ramadan Trust Initiative da ke Masallacin juma’a na Alfurkan dake Kano Alhaji Kabiru Isyaku, ya yi kira ga al’ummar musulmi da su tashi tsaye wajen tallafawa mabukata musamman ma a wannan lokaci da muke dab da shiga watan azumin Ramadan.
Alhaji Kabiru Isyaku ya bayyana hakan ne a jiya, yayin wani taron shekara-shekara da kungiyar ta saba gudanarwa domin tattaunawa kan yadda gidauniyar za ta tallafawa mabukata a lokacin Azumi.
Ya ce kasancewar Azumin watan Ramadan yana dab da shigowa akwai bukatar tunatar da al’ummar musulumi muhimmancin taimakawa marasa galihu.
Alhaji Kabiru Isyaku ya kara da cewa gidauniyar za ta ci gaba da zuwa gidajen marayu na Kano da Asibitoci da gidan gyaran hali domin tallafawa mabukata.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito shugaban gidauniyar na cewa, taimakawa marasa galihu zai taimaka gaya wajen rage talauci tsakanin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login