Labarai
Kotu a Kano ta yanke wa Baturen da ya kade Bahaushe a mota hukunci
Babbar kotun jiha mai lamba 11 a nan Kano ta yanke wa wani Bature biyan kudi har Naira miliyan 13 ga matashin da ya kade da Mota lokacin da yake sauri, a wani mumunan hatsari da ya afku a titin rukunin masana’antu na Sharada.
A ranar Talata ne kotun ta kawo karshen shari’ar Baturen mai suna John Bouton dake aiki a wani kamfani dake rukunin masana’antu na Sharada dake Kano.
An tuhumi Baturen ne da laifin yin awon gaba da matashin yayin da yake tafiya a kafa, a cikin shekarar 2015, wanda ya sanya matashin ya shigar da kara a kotun.
Karin labarai:
Yanzu-yanzu: Kotu ta dakatar da Anti-Corruption daga bincikar Sarkin Kano
Kotu ta shawarci masu zuba hannun jari a Kano
Da yake yanke hukunci, mai Shari’a Rabi’u Abubakar Sadiq ya ce Baturen John Bouton zai biya Naira Miliyan 13 kuma za a bayar da Miliyan 5 da dubu dari nan take, sai kuma cikon miliyan 8 da za a rika biya a duk wata ga matashin.
Bayan fitowa daga kotun Freedom Radio ta zanta da lauyan mai kara Abdul Adamu Fagge wanda ya ce yayi farin ciki da wannan nasara da suka samu a shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login