Labarai
Kotu ta bai wa EFCC damar ci gaba da tsare Godwin Emefiele
Babbar kotu a Ikeja da ke birnin Lagos, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele.
Kotun, ta bai wa hukumar EFCC damar ci gaba da tsare Mista Godwin Emefiele har zuwa ranar 11 ga watan nan da muke ciki na Afrilu da za ta yanke hukunci kan yiwuwar bayar da shi beli.
Yayin zaman kotun dai, tsohon gwamnan babban bankin, ya musanta sababbin tuhume-tuhumen da ake masa na karya dokokin da suka shafi hada-hadar kuɗaɗen kasashen waje da hukumar EFCC ke masa.
BBC ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta zargi Godwin Emefiele da ware wasu kuɗaɗen waje kusan Dala biliyan biyu ba tare da bin ka’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login