Labaran Kano
Kotu ta dakatar da jagororin NALCOF reshen jihar Kano
Kotun Majistare ƙarkashin mai shari’a Tijjani Saleh Minjibir, mai lamba 60 a gidan Murtala dake Kano ta dakatar da shugabannin ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon kafa rukuni na ɗaya ta ƙasa wato (NALCOF), sakamakon ƙarewar wa’adin su.
Tun da farko wasu mutane huɗu Dauda Auwalu Zage da Aminu Abba Ƙwaru da Auwalu Salisu sai Mu’awiyya Adamu, sun shigar da ƙara tare da neman dakatar da tsagin shugabancin da wa’adin su ya ƙare, kan su bada ikon gudanar da komai da ke hannun su ga shugaban gudanar da zaɓe na sabbin jagororin ƙungiyar.
Waɗanda ake ƙara sun haɗa da, ƙungiyar ta NALCOF, sai Faruk Ibrahim da Aliyu Kassim sai Salisu Ibrahim Danladi da Auwalu Saminu tare da Sani Isyaku Dogo da Salisu Usman sai Muzammil Ɗalha Yola da Shehu Muhammad Yellow da Ujudu Muhammad S/Fada.
Bayan dakatarwar kotun ta umarci waɗanda ake ƙara da su daina nuna kan su a matsayin jagororin ƙungiyar kasancewar hakan ya saɓa ka’ida, sakamakon ƙarewar wa’adin mulkin su tun ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2015.
Kotun ta ɗage zaman sauraron shari’ar har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login