Labarai
Kotu tayi watsi da bukatar soke sabbin masarautu
Babbar kotun jihar Kano ta kori karar da masu zabar sarki na masarautar Kano suka shigar suna kalubalantar kirkirar sabbin masarautu guda hudu da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Da yake yanke hukunci a safiyar yau litinin, mai shari’a Ahmed Tijjani Badamasi ya kara tabbatar da hukuncin da mai shari’a Usman Na’aba ya yi a ranar 21 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata na tabbatar da masarautun.
Majalisar dokoki ta Kano ta amince da dokar kafa masarautu 4
Ganduje ya sakawa dokar kikiro masarautu hannu
Kotu ta dage sauraran karar dattawan Kano kan sabbin masarautu
Idan za’a iya tunawa masu nada sarki a masarautar Kano wanda suka hada da Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Yusuf Nabahani , da Makaman Kano kuma hakimin Wudil Abdullahi Sarki-Ibrahim da sarkin Dawaki Mai Tuta kuma hakimin Gabasawa Bello Abubakar da sarkin ban Kano hakimin Dambatta Muktar Adnan sune suka shigar da karar suna kalubalantar kirkirar sabbin masarautun.