Labarai
Koyi da bakin al’adu shi ke kawo mutuwar aure a Najeriya
Shugaban cibiyar wayar da kan al’umma da karfafa musu gwiwa kan zamantakewa malam Auwal Salisu ya ce rashin bin koyarwar addinin islama da bijirewa al’adun bahaushe da koyi da bakin al’adu na bayar da gudunmuwa wajen tabarbarewar aure.
Malam Auwal Salisu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na Freedom radio wanda ya mayar da hankali kan taron da cibiyar ta gudanar a ranar asabar din da ta gabata don wayar da kan al’umma kan zamantakewar aure.
Shugaban ya kuma kara da cewar babban abinda ke kawo mutuwar aure a wannnan lokaci rashin gina aure akan gaskiya wanda hakan shine ke haifar da matsalar.
A nasa bangaren Malam Tijjani Muhammad Musa ya bayyana cewar iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar aure da rashin dora yaransu hanyar da ta dace.
Tijjani Muhammad Musa ya kara da cewar duk wanda suka kasance miji da mata su sauke girman kai da wasu dabi’u wanda suke kara kawo matsala a zamantakewa.
Bakin sun kuma bukaci iyaye su kasance masu koyawa ‘ya’yan su ilimin zamantakewar aure kafin aurar da su tare da nusar dasu hanyoyin da zasu girmama junan su a matsayin ma’aurata.
You must be logged in to post a comment Login