Labarai
Kungiyar ma’aikatan lantarki sun garkame ofishin KEDCO
Kungiyar ma’aikatan dake samar da wutar lantarki ta kasa ta tsunduma a yajin aikin sai baba ta gani a yau.
Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan dake Samar da wutar lantarki ta kasa shiyar arewa maso yamma kwamared Muhammad Musa, ne ya bayyana haka ya yin da yake zantawa da manema labarai a yau.
Kwamared Muhammad Musa, yace sun dauki matakin ne sakamakon Gaza biya musu bukatun su da kamfanonin da suke yiwa aiki su.
Ya kuma ce akwai ma’aikatan da suka bar aiki sama da dubu biyu wanda har ya zuwa yanzu an gaza biyan su hakkokin su na barin aiki duk da cewa sun mika korafe-korafen su ga ministan samar da wutar lantarki na kasa.
A nasa bangaren shugaban kungiyar reshen jihar Kano, kwamared Auwal Musa Muhammad, cewa yayi sun dauko matakin tsunduma yajin aikin ne sakamakon mawuyacin halin da tsafafin ma’aikatan kungiyar ke ciki da iyalansu bisa gaza biyan su hakkokin su.
Kungiyar Rumbun abinci na taimakawa yara masu tamowa da abincin gina jiki a Kano
Kungiyoyin manoma ku biya bashin da ake bin ku -CBN
Kungiyar kishin al’ummar Kano za ta gina cibiyar fasaha
Jami’in hulda da jama’a na kamfanin rarraba hasken wutar lantarki shiyar Kano da jigawa da Kuma katsina, Ibrahim Sani Shawai, ya ce yajin aikin kungiyar ma’aikatan bai shafi kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ba Kuma za su cigaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda suka Saba.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito cewa kungiyar ma’aikatan dake samar da hasken wutar lantarki ta garkame babbar shalkwatar offishin dake nan Kano.