Coronavirus
COVID-19: Kusan mutane dubu 4 sun mutu a kwana daya a kasar Indiya

Akalla mutane dubu uku da dari bakwai da tamanin ne suka mutu a kasar Indiya a jiya talata sakamakon cutar corona.
Wannan adadi dai shine mafi yawa da kasar ta Indiya ta fuskanta tun bayan bullar cutar covid-19 a kasar
Ya zuwa yanzu dai sabbin wadanda suka kamu da cutar sun kai dubu dari uku da tamanin da biyu.
Sai dai masana harkokin lafiya a kasar sun yi hasashen cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya fi yadda gwamnati ke sanarwa domin kuwa akwai wasu da dama da cutar ta hallaka wadanda ba a dau alkalumansu ba.
You must be logged in to post a comment Login