Labarai
Kwamishinan mata ta sha alwashin dakile shaye-shayen kwayoyi a Kano
Kwamishinan mata ,walwala da cigaba ta jihar Kano Dr Zahra’u Muhammad Umar ta sha alwashin kawo karshen matsalar shaye-shayen kwayoyi da cin zarafin mata, da kuma matsaloli na yawaitar tallace-tallace a fadin jihar.
Kwamishinan ta bayyana haka ne a wata takarda da sa hannun jami’ar hulda da jama’a na ma’aikatar Hadiza Mustapha Namadi a ma’aikatar a jiya.
Kwamishinan ta bayyana wannan kudiri nata ne jim kadan bayan da ta fara aiki a ofishin ta a jiya laraba , kwana daya bayan kaddamar da su da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yayi tare da wasu kwamishinonin su goma sha tara.
Ta bayyana cewar cigaban al’umma na daya daga cikin muhimman kudoririn gwamnatin jihar Kano, inda ta kara da cewa babban burinsu bai wuce jihar Kano ta kasancewa jihar da ta fi kowacce jiha samu nasarori a fadi kasar nan ba.
NCDC:An samu karin mutane 37 da suka kamu da zazzabin lassa
Ta ce za’a samu haka ne kadai ta hanyar bada hadin kai daga bangaren dukkanin wadanda suke da madafin iko a wannan mulki.
Da yake Magana babban sakataren ma’aikatar Auwalu Umar Sanda wanda ya karbi kwamishinar ya sha alwashin ba ta dukkanin hadin kan da ya dace wajen tafiyar da aikin yadda ya kamata.
Mal Sanda ya ce ma’aikatar ke da alhakin tafiyar da dukkanin gidajen marayu da gajiyayyu musammam gidan marayu dake Nassarawa,gidan masu tabin hankali