Connect with us

Labarai

REMASAB ta yi aikin tsaftar muhalli a Cibiyar horas da jami’an tsaro ta Gabasawa

Published

on

Hukumar kula da shara da tsaftar muhalli ta Kano, REMASAB, ta gudanar da aikin tsaftar muhalli a harabar Cibiyar horar da jami’an tsaro da ke ƙaramar hukumar Gabasawa.

Aikin ya haɗa da yanke ciyawa da fesa maganin kashe ƙwari, domin tsaftace harabar makarantar da inganta yanayin muhalli, a wani mataki na ƙoƙarin farfaɗo da cibiyar tare da inganta ta.

 

Sanarwar da jami’in yada labaran hukumar Abubakar Ahmad Durumin Iya, ya fitar mai dauke da sa hannun sa , ya ce a halin yanzu cibiyar ba ta aiki, yayin da aikin tsaftar muhalli ke daga cikin shirye-shiryen gyara harabar da kuma yiwuwar sake buɗe makarantar.

Da ya ke karin haske kan aikin, shugaban hukumar ta REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ya ce matakin ya yi daidai da ƙudirin hukumar na inganta tsaftar muhalli da kuma tallafa wa ƙoƙarin farfaɗo da cibiyoyin gwamnati a jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!