Labarai
Wata ambaliyar ruwa a Jalingo babban birnin jihar Taraba ta yi mummunar barna

Ambaliyar ruwa a Jalingo babban birnin jihar Taraba ya yi sanadiyyar rushewar gidaje da kuma shafe kadarori da dama.
Rahotanni sun ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara tun ƙarfe 2:30 na dare zuwa 11:30 na safiyar jiya Asabar ne ya yi sanadin ambaliyar da Rahotanni suka tabbatar da cewa ta shafi unguwannin Mile Six, Mafindi da kuma Mayogwai, sai kuma babbar kasuwar Jalingo da ruwan ya shafe shaguna.
Mazauna yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun shaidawa manema labarai cewa ta faru ne a sakamakon toshewar magudanan ruwa.
Bayanai sun nuna cewa ambaliyar ta kuma haddasa cunkoson ababen hawa a kan babbar hanyar Jalingo zuwa Wukari sakamakon yadda ta haɗu da aikin sabuwar gada da ake ginawa.
Wannan shine karo na biyu cikin makonni uku da ruwan sama ke dakatar da aikin ginin gadar.
You must be logged in to post a comment Login